Falasdin ta ki karbar kayan taimakon yaki da Corona daga hannun HDL

Gwamnatin Falasdin ta ki karbar kayan taimakon yaki da annobar Corona da Hadaddiyar Daular Larabawa ta aika mata ta hanyar kasar Isra'ila.

1421323

Ministan Lafiya na Falasdin Mey Keyle a wajen wani taro kan yaki da Corona da aka gudanar a garin Baytullahim na Yammacin gabar Kogin Jordan ya shaida cewar "Hadaddiyar Daular Larabawa ba ta yi magana da mu kan za ta aiko da kayan taimako ba. A saboda haka mun mayar mata da su ba ma so."

Keyle ya jaddada cewar Falasdin kasa ce mai cin gashin kanta, kuma duk abunda za a yi sai an tuntube su tare da hada kai da su.Labarai masu alaka