Turkiyya ta aike da sakon ta'aziyya ga Nijar

Turkiyya ta aike da sakon ta'aziyya ga Nijar sakamakon sojojin da aka kashe a harin ta'addanci a kasar

1420909
Turkiyya ta aike da sakon ta'aziyya ga Nijar

Turkiyya ta aike da sakon ta'aziyya ga Nijar sakamakon sojojin da aka kashe a harin ta'addanci a kasar.

Rubutacciyar sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Waje ta Turkiyya ta fitar ta ce, sun yi matukar bakin ciki da samun labarin harin ta'addancin da aka kai a garin Diffa inda aka kashe sojojin kasar.

Sanarwar ta ce "Muna sukar wadannan munanan hare-hare na ta'addanci. Muna Addu'ar samun jin kan Allah ga wadanda suka mutu da saukin cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata. Muna mika ta'aziyya ga gwamnati da al'ummar Nijar baki daya.

Sojoji 12 aka kashe sakamakon harin da 'yan ta'addar Boko Haram suka kai a sansanin soji na Blabrine da ke garin Diffa a ranar Litinin din da ta gabata.Labarai masu alaka