Kwamiti ta amince da Ratcliffe a matsayin daraktan leken asirin Amurka

Kwamitin leken asiri a majalisar dattijan Amurka ta amince da John Ratcliffe a matsyar daraktan Hukumar Kula da Sirri ta Kasa (DNI) da shugaba Donald Trump ya zaba

1420403
Kwamiti ta amince da Ratcliffe a matsayin daraktan leken asirin Amurka

Kwamitin leken asiri a majalisar dattijan Amurka ta amince da John Ratcliffe a matsyar daraktan Hukumar Kula da Sirri ta Kasa (DNI) da shugaba Donald Trump ya zaba.

Ratcliffe, wanda ke wakiltar Texas a Majalisar Wakilai, ya samu amincewa kwamitin lejken asirin a majalisar dattijai bayan kuri'ar da aka kada.

A kuri’ar, sanatocin Jam’iyyar Republican 8 suka amince da shi inda 7 na Democrat suka ce “a’a”

Ratcliffe zai fara aikinsa idan har aka amince da shi a kuri’ar da za'a kada a babban taro na majalisar dattijai a cikin kwanaki masu zuwa.

 Labarai masu alaka