Trump: Idan Iran ta kai mana hari a Iraki za ta gane kurenta

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewar sun samu bayanan sirri dake nuna Iran na shirin kaiwa sojojin Amurka hari a IrakShugaban Kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewar sun samu bayanan sirri dake nuna Iran na shirin kaiwa sojojin Amurka ha

1389679
Trump: Idan Iran ta kai mana hari a Iraki za ta gane kurenta

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewar sun samu bayanan sirri dake nuna Iran na shirin kaiwa sojojin Amurka hari a Iraki, kuma idan haka ta faru to za su mayar da martani kakkausa.

Donald Trump ya fitar da wata sanarwa ta shafinsa na Twitter inda ya yi bayanai game da Iran cewa "Bayanan da suka zo mana na nuna cewar Iran ko kuma kawayenta na shirin kai mana hari ko kaiwa kayanmu dake Iraki. Idan har haka ta faru, to tabbas Iran za ta danana kudarta."

Trump bai bayar da wani dogon bayani ba kan wanne irin bayanan sirri suka samu ba game da shirin kai musu hari a Iraki.

A farkon watan Janairu Amurka ta kashe Kwamandan Sojin Juyin Juya Hali na Iran Kasim Suleymani a wani hari ta sama da ta kai a Iraki, hakan ya sanya Iran ke kai harin martani kan sansanonin Amurka dake kasar ta Iraki.Labarai masu alaka