Fararen hula 707 aka kashe a Siriya a watanni 3 na farkon 2020

A watanni 3 na farkon wannan shekarar ta 2020 fararen hula 707 aka kashe a Siriya.

1389200
Fararen hula 707 aka kashe a Siriya a watanni 3 na farkon 2020

A watanni 3 na farkon wannan shekarar ta 2020 fararen hula 707 aka kashe a Siriya.

Rundunar Kare Hakkokin Dan Adam ta Siriya (SNHR) ta ce a watan Maris kadai an kashe fararen hula 145 a kasar sakamakon hare-haren da aka kai.

A rahoton da Rundunar SNHR ta fitar na watan Maris an bayyana cewar a watan na Maris da ya gabata an kashe fararen hula 145 da suka hada da mata 16 da yara kanana 28 sakamakon hare-haren da aka kai.

Dakarun gwamnatin Siriya da suka hada da na Assad da na 'yan ta'adda 'yan kasashen waje Iran ke goyawa baya sun kashe fararen hula 36 da suka hada da mata 3 da yara kananan 5 a wannan lokaci.

A hare-haren da jiragen saman Rasha suka kai kuma an kashe fararen hula 19 da suka hada da mata 7 da yara kanana 2. 'Yan ta'addar aware na PKK/YPG kuma sun kashe fararen hula 12 da suka hada da yara 2.

mayaka masu adawa da gwamnatin Siriya sun yi musabbabin mutuwar fararen hula 2, sauran bangarori kuma sun kashe fararen hula 76 da suka hada da yara kanana 19 da mata 7.

A wannan shekarar a kasar Siriya a watan Janairu an kashe fararen hula 286, a Fabrairu 276 sai a Maris 145 wanda adadin ya kama 707.

Rahoton Rundunar ta SNHR ya ce daga cikin mutanen da aka kasheawatan da ya gabata akwai 12 da aka dinga azabtar da su har suka mutu.Labarai masu alaka