Turkiyya ta soki hare-haren ta'addanci da aka kai a Afganistan

Turkiyya ta la'anta tare da sukar hare-haren ta'addanci da aka kai a Afganistan.

1388061
Turkiyya ta soki hare-haren ta'addanci da aka kai a Afganistan

Turkiyya ta la'anta tare da sukar hare-haren ta'addanci da aka kai a Afganistan.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar da sanarwar cewa "Mun yi bakin ciki da samun labarin mutuwar jami'an tsaro da dama a hare-haren ta'addanci da a aka kai a jihohin Takhar, Zabul, Helmand da Baghlan dake Afganistan. Muna la'antar wadannan hare-hare, muna Addu'ar Allah Ya ji kan wadanda suka mutu da kuma fatan sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata. Turkiyya na mika sakon ta'aziyya ga dukkan al'umar Afganistan."

Jami'an tsaro 25 ne suka mutu sakamako hare-haren ta'addanci da kungiyar Taliban ta kai a jihohin Tahar da Zabul da kuma arangamar da 'yan ta'addar na Taliban suka yi da jami'an tsaro a jihar Baghlan.

Afganistan ta jima tana fuskantar hare-haren 'yan ta'addar Taliban wadanda ke kai wa jami'an tsaro farmakai. A wasu lokutan suna kashe fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba.

Amurka tare a hadin gwiwar gwamnatin Afganistan na kokarin ganin an cimma sulhu da Taliban inda a kwanakin baya Shugaban Amurka Donald Trump ya tattauna da wasu shugabannin kungiyar.Labarai masu alaka