Sama da mutane dubu 35 sun koma matsugunansu a Idlib

Sakamakon cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da gwamnatocin Turkiyya da Rasha suka cimma kuma ta fara aiki a ranar 6 ga watan Maris, mutane sama da dubu 35 da suka rasa matsugunansu sun koma gidajensu dake Idlib.

1387723
Sama da mutane dubu 35 sun koma matsugunansu a Idlib

Sakamakon cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da gwamnatocin Turkiyya da Rasha suka cimma kuma ta fara aiki a ranar 6 ga watan Maris, mutane sama da dubu 35 da suka rasa matsugunansu saboda hare-haren gwamnatin Asad da masu goya mata baya a yankin da aka hana rikici a cikinsa na Idlib sun koma gidajensu.

Daraktan Wata Cibiya dake Kula da Alkaluma Gudun Hijira a Siriya Muhammad Hallaj ya bayyanawa duniya cewar , sakamakon dakatar da kai hare-hare da gwamnatin Asad da masu taimaka mata suka yi, da kuma aiki da yarjejeniyar tsagaita wani bangare na fararen hula sun koma gidajensu.

Hallaj ya ce "Daga watan Oktoban 2019 zuwa yau da gwamnatin Siriya ta tsaurara kai hare-hare zuwa yau sama da fararen hula miliyan 1 sun rasa matsgunansu. Bayan tsagaita wutar sama da farare hula dubu 35 sun koma gidajensu."

Hallaj ya ci gaba da cewar sakamakon mamayar yankunan Idlib ta kasa da dakarun gwamnatin Siriya suka yi, sun kwace yankunan fararen hula da dama, kuma akwai dubunnan daruruwan fararen hular da sun hakura da komawa yankunansu saboda hare-haren gwamnati kuma wasunsu suna rayuwa a sansanonin 'yan gudun hijira dake iyakar Turkiyya da Siriya.

Darakta Hallaj ya ce ya bukaci wadanda suka koma gidajen nasu da su kula da bama-baman da ba su fashe ba kuma su sanar da mahukunta da zarar sun ga wani abu mai halakarwa.Labarai masu alaka