Faransa ta janye sojojinta daga Iraki

An bayyana cewar Faransa ta janye sojojinta daga sansanin sojojin kawancen kasashen duniya da ke yaki Daesh wadanda Amurka ke jagoranta a kasar Iraki.

1385359
Faransa ta janye sojojinta daga Iraki

An bayyana cewar Faransa ta janye sojojinta daga sansanin sojojin kawancen kasashen duniya da ke yaki Daesh wadanda Amurka ke jagoranta a kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labarai na INA ya bayyana cewar, Kakakin sojin Iraki Abdulkarim Halif da ya yi aiki karkashin Firaministan kasar Abdulmahdi wanda sakamakon zanga-zanga ya yi murabus a  ranar 29 ga Nuwamba ya ce, yarjejeniyar da aka kulla da Faransa ta zo karshe wadda ta tanadi cewar bayan an gama yaki da Daesh sojojinta za su bar kasar.

Halif bai bayar da wani dogon jawabi ba game da dalilin janyewar sojojin na Faransa daga Iraki.

Ma'aikatar Tsaro ta Chek a ranar Larabar nan ta bayyana cewar ta janye sojojinta daga Iraki sakamakon yaduwar cutar Corona (Covid-19) da kuma yawaitar hare-haren da ake kai wa a kasar.Labarai masu alaka