Amurka za ta binciki gwamnatin China game da sakaci kan Corona

An gabatarwa da Majalisar Dokokin Amurka wani kudiri inda aka bukaci da a binciki gwamnatin Beijing game da sakaci kan cutar Corona (Covid-19) da ta fara bulla a garin Wuhan na China.

1384640

Dan majalisar dokokin Amurka na jam'iyyar Republican Josh Hawley da ta majalisar wakilai Elise Stefanik ne suka gabatar da kudirin inda suka soki China kan sakaci ga mutanen da aka samu dauke da cutar tun farko.

A kudirin nasu sun ce "Suna so a bayyanawa duniya irin illar da boye bayan da China ta yi kan cutar. Haka zalika sun bukaci da a biya diyya ga dukkan kasashen da aka samu bullar cutar a cikinsu.

Hawley ya bayyana cewar tun farkon fara bullar cutar China ta dinga yi wa duniya karya.

Ya ce "China ta fadi cewar ta gano cutar ne tun farkon watan Disamba amma ta bayar da umarnin a goge dukkan sakamakon da aka samu a dakunan bincike. Ta kuma taura likitoci kan su yi shiru."

Stefani kuma cewa ta yi boye bayanan da Chiina ta yi ne ya janyo mutuwat dubunnan mutane a duniya da suka hada da Amurkawa. A saboda haka dole ne a bincike gwamnatin China kan wannan abu da ta yi.Labarai masu alaka