Pompeo: Hamaney na boyewa duniya gaskiya game da Corona a Iran

Ministan Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo ya bayyana cewar Shugaban Addini na Iran Ayatullah Ali Hamaney na boyewa duniya gaskiya game da annobar Corona (Covid-19) a kasarsa.

1383825
Pompeo: Hamaney na boyewa duniya gaskiya game da Corona a Iran

Ministan Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo ya bayyana cewar Shugaban Addini na Iran Ayatullah Ali Hamaney na boyewa duniya gaskiya game da annobar Corona (Covid-19) a kasarsa.

Pompeo ya fitar da wata sanarwa mai taken "Karyar da Hamaney ke yi na jefa rayuwar mutane cikin halaka."

A sanarwar, Pompeo ya ce za su fada wa duniya gaskiya game da abubuwan da Hamaney yake boyewa kan "Cutar Wuhan".

Pompeo ya kuma ce a watan da ya gabata kamfanin jiragen saman Iran na Mahan Air ya yi safara sau 55 zuwa tsakanin Tehran da China, ya kuma zargi Iran da jefa ruyuwar miliyoyin mutane cikin halaka.

Ya ce "Iran ta gargadi ma'aikatan lafiyarta, kuma sai bayan kwanaki 9 da fara samun mutuwa daga Corona sannan ta fara sanar da duniya. Iran na ci gaba da yi wa duniya karya game da kamuwa da Corona da kuma adadin wadanda ta kashe a kasar. Abun bakin ciki ne kan yadda adadi na gaskiya ya haura wanda gwamnatin Iran ke fada."

Pompep ya kuma zargi Iran da kashe wa aiyukan ta'addanci kudi har dala biliyan 16 daga shekarar 2012 zuwa yau.

Ya kuma ce gwamnatin Iran ta sace Yuro biliyan 1 da ya kamata a yi amfani da shi wajen kula da lafiya a kasar. Haka zalika a yanzu ma tana boye abubuwan rusfe fuska, safar hannu da magunguna don sayarwa da kasashen waje ta bayan fage.

Mike Pompeo ya kuma jaddada cewar takunkumin da Amurka ta saka wa Iran bai shafi kayan abinci, kayan taimakon jin kai da magunguna ba, kuma tun daga watan Janairu zuwa yau kamfanunnukan lafiya na Iran za su iya sayen kayan gwajincutar Corona tare da kai su kasar.

Pompeo yatunatar da cewar sun ware dala biliyan 100 don bayar da taimako ga kasashen duniya da suka hada da Iran amma Hamaney ya nuna ba sa bukata inda yake ci gaba da kirkirar karya don batawa Amurka suna.Labarai masu alaka