Jamus ta kara wa'adin dakatar da sayarwa da Saudiyya makamai

Jamus ta kara wa'adin watanni 9 na dakatar da sayarwa da Saudiyya makamai.

1383778
Jamus ta kara wa'adin dakatar da sayarwa da Saudiyya makamai

Jamus ta kara wa'adin watanni 9 na dakatar da sayarwa da Saudiyya makamai.

Kamfanin dillancin labarai na DPAdake Jamus ya rawaito kakakin gwamnatin Jamus na cewar gwamnatin kasar ta kara wa'adin dakatar da sayarwa da Saudiyya makamai har nan da watan Disamban 2020.

Sanarwar da aka fitar ta ce "A bisa doka, duk bukatar sayen makamai da Saudiyya ta mika har nan da watan Disamban 2020 ba za a amince da ita ba.", kuma ya zuwa wannan lokaci za a dakatar da bayar da makaman da aka amince a saye su.

Sakamakon kisan dan jarida Jamal Kashoggi ne Jamus ta dakatar da sayarwa da Saudiyya makamai a watan Nuwamban 2018, an kara wa'adin daga watan Satumban 2019 zuwa Maris din 2020, wanda a yanzu aka sake kara shi zuwa karshen shekarar.

A gefe guda, kawancen da jam'iyyar CDU mai mulkin Jamus ta kulla da jam'iyar SDP ya amince da kar a sayar da makamai ga bangarorin da suke rikici da juna a Yaman.Labarai masu alaka