Ruhani: Makiricin makiya ne ke kara tsoratar da Iraniyawa game da Corona

Shugaban Kasar Iran Hasan Ruhani ya bayyana cewar "Makircin Makiya ne" ke yada tsoro da fargaba game da cutar Corona (Covid-19).

1366513

Bayan taron da aka gudanar a Cibiyar Yaki da Corona dake Tehran, Ruhani ya bayani ga manema labarai game da matakan da suka dauka don magance cutar da ta bulla a kasarsa.

Ruhani ya ce, da fari an samu yawaitar jama'a a asibitoci amma daga baya hakan ya ragu, kuma an samu nasarar yi wa mutane da dama magani.

Ya ce "Dole dukkan hukumomi su kula. Makircin makiya ne ke kokarin yada tsoro da fargaba tare da durkusar da kasar. Kowa ya ci gaba da aiyukansa yadda ya dace."

Ma'aikatar Lafiya ta Iran ta sanar da mutuwar murane 15 daga cikin 95 da cutar corona ta kama.Labarai masu alaka