Isra'ila na ci gaba da ruwan bama-bamai a Zirin Gaza

Jiragen sama na yaki mallakar Isra'ila na ci gaba da yin ruwan bama-bamai a yankin Zirin Gaza da Yahudawa suka yi wa kawanya.

1365744
Isra'ila na ci gaba da ruwan bama-bamai a Zirin Gaza

Jiragen sama na yaki mallakar Isra'ila na ci gaba da yin ruwan bama-bamai a yankin Zirin Gaza da Yahudawa suka yi wa kawanya.

Isra'ila ta nufi matsugunai daban-daban na mayakan Saraya Al-Kudus, reshen soji na kungiyar Jihad Islam dake Zirin Gaza.

Kungiyar Saraya Al-Kudus ta ce ta fara kai hare-hare da makaman roka don mayar da martani ga Isra'ila.

Kakakin Saraya Al-Kudus mai suna Abu Hamza ya fitar da sanrmarwa ta shafinsa na Twittet cewa "Mun sanar da dakatar da kai harin martani kan Isra'ila saboda hare-haren da ta kai Gaza da Sham, amma makiyanmu sun ki cika alkawari inda suka kai wa matsugunanmu hari. Mu ma za mu ci gaba da mayar da martani."

Rikici Tsakanin Isra'ila da Gaza ya tsananta bayan da sojojin Isra'ila suka kashe wani mamban kungiyar Jihad Islam da safiyar Litinin din nan.

An harba makaman roka sama da 49 zuwa Isra'ila daga Gaza, wanda hakan ya sanya Israilan yin ruwan bama-bamai kan sansanonin Jihad Islam dake Gaza da Sham Babban Birnin Siriya.

Sakamakon hare-haren an kashe mayakan Jihad Islam 2 a Siriya inda aka jiknata wasu 4 a Zirin Gaza.

 Labarai masu alaka