Masu ra'ayin mazan jiya sun lallasa masu ra'ayin kawo canji a zaben 'yan majalisun kasar Iran

An bayyana cewar a zaben 'yan majalisun kasar Iran da zasu kafa majalisa ta 11 a kasar jam'iyyar masu ra'ayin mazan jiya sun lashe kujeru 195 daga cikin kujeru 253 inda suka barwa masu ra'ayin kawo canji kujeru 18

1364527
Masu ra'ayin mazan jiya sun lallasa masu ra'ayin kawo canji a zaben 'yan majalisun kasar Iran

An bayyana cewar a zaben 'yan majalisun kasar Iran da zasu kafa majalisa ta 11 a kasar jam'iyyar masu ra'ayin mazan jiya sun lashe kujeru 195 daga cikin kujeru 253 inda suka barwa masu ra'ayin kawo canji kujeru 18.

Dangane da bayanan da suka fito daga Hukumar Zaben kasar an bayyana sakamakon zabukan yankuna 171 daga cikin 208.

Dangane da labaran da kafafen yada labaran cikin gidan kasar suka rawaito daga cikin kujerun da aka bayyana jam'yyar masu ra'ayin mazan jiya sun lashe kujeru 195 inda masu ra'ayin kawo sauyi suka samu kujeru 18, yan takara masu zaman kanmsu kuwa suka samu kujeru 40.

 Labarai masu alaka