Trump zai hana bayar da Visar Amurka ga 'yan Najeriya

Gwamnatin Amurka karkashin Donald Trump na shirin samar da wata sabuwar doka don hana 'yan kasashen duniya 7 Visar shiga kasar.

Trump zai hana bayar da Visar Amurka ga 'yan Najeriya

Gwamnatin Amurka karkashin Donald Trump na shirin samar da wata sabuwar doka don hana 'yan kasashen duniya 7 Visar shiga kasar.

Labaran da jaridun Amurkasuka fitar na cewar kasashen da wannan doka za ta shafa sun hada da Belarus, Eritiriya, Kirgizistan, Myammar, Najeriya, Sudan da Tanzaniya.

Wani babban jami'in Fadar White House ya ce har yanzu ba a gama tattara sunayen kasashen ba amma akwai yiwuwar a kara wata kasa a ciki.

Sabuwar dokar ba za ta hana dukkan 'yan wadannan kasashe shiga Amurka ba amma za a tsaurara ka'idoji wajen ba su Visar yawon bude ido, kasuwanci da kuma izinin zama a kasar.

A gefe guda an bayyana cewar ba a gama fitar da dokar ba, kuma da zarar an kammala Fadar White House za ta fitar da sanarwa.

A ranar 27 ga watan Janairun 2017 ma Trump ya samar da dokar hana izinin shiga Amurka ga 'yan kasashen Iran, Siriya, Libiya, Yaman, Somaliya, Cadi da Koriya ta Arewa.Labarai masu alaka