Sarauniyar Ingila Elizabeth II ta amince da dokar Brexit

Sarauniyar Ingila Elizabeth II ta amince da dokar ficewar kasar daga Tarayyar Turai (Brexit) wanda majalisar ta kada kuri'ar za ta fara aiki daga ranar 31 ga watan Janairu.

Dokar ta samu amincewa cikin sauri a karamar majalisar amma ta fuskanci kalubale a babbar majalisa wanda hakan ya sanya aka sake mayar da ita.

Firaminista Boris Johnson ya yi amfani da damar rinjayen da yake da shi a karamar majalisar inda ya sake mayar da dokar babbar majalisa.

Yarjejeniyar da Ingila da Tarayar Turai suka kulla ta tanadi cewar kasar za ta ci gaba da zama da aiyuka da Tarayyar har nan da 31 ga Janairu, amma kuma ba za ta shiga harkokin siyasarta ba. A wannan lokaci za su samar da yarjejeniyar kasuwanci ba tare da tsangwama ba da zai yi wa kowa dadi.

Amma Firaminista Johnson ya ce ko sun cimma wata yarjejeniya ko ba su cimma ba za su fice daga Tarayar Turai a ranar 31 ga watan Disamba.

A shekarar 2016 ne al'umar Ingila suka jefa kuri'ar jin ra'ayin jama'a kan Brexit inda kaso 52 suka amine da a fice, yayinda kaso 48 suka nuna a zauna.Labarai masu alaka