Maduro ya bukaci MDD ta tura masu sanya idanu a lokacin zaben 'yan majalisar Venezuela

Shugaban Kasar Venezuela Nicolas Maduro ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta aike jami'a masu sanya idanu a lokacinda za a gudanar da zaben Majalisar Dokokin kasar dake hannun 'yan adawa.

A jawabinda Maduro ya yi a wajen wani taro da aka gudanar a Caracas Babban Birnin Venezuela ya soki madugun 'yan adawa Juan Guaido da ya aiyana kansa a matsayin shugaban wucin gadi.

Maduro ya zargi 'yan adawar da kawo wa kasar takunkumai da rigingimu, kuma yana sn MDD ta tura masu sanya idanu a loakcinda za a gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin Venezuela a wannan shekarar.

Maduro ya zargi Guaido da kalmashe taimakon dala miliyan 435 da Amurka ta bayar don taimakon jinkai.Labarai masu alaka