An kashe mambobin Hizbul Mujahidun 3 a Kashmir

Sakamakon wani mummunan rikici da aka fafata tsakanin jami'an tsaro da 'yan tawaye a yankin Jammu Kashmir na Indiya an kashe mambobin kungiyar Mujahidun 3.

Tashar talabijin ta NDTV ta bayyana cewar bayan 'yan sanda sun samu rahotannin sirri ne suka kewaye yankin Shopian tare da gudanar da bincike.

'Yan sanda sun bayyana cewar an kashe mambobin kungiyar Hizbul Mujahidun 3 a arangamar da aka yi, kuma 1 daga cikin wadanda aka kashe tsohon dan sanda ne da ya bar aiki a 2018 tare da shuga kungiyar.

Yankin Jammu Kashmir ya dade yana fama da rikici.Labarai masu alaka