Sanarwar bayan Babban Taron Kasashen Duniya game da Libiya

An fitar da sanarwar Bayan Taron neman tabbatar da tsagaita wuta da zaman lafya a Libiya wanda aka gudanar a Berlin Babban Birnin Jamus.

1343778
Sanarwar bayan Babban Taron Kasashen Duniya game da Libiya

An fitar da sanarwar Bayan Taron neman tabbatar da tsagaita wuta da zaman lafya a Libiya wanda aka gudanar a Berlin Babban Birnin Jamus.

Sanarwar bayan taron ta bayyana cewar, wakilan Libiya sun amince da bayar da goyon baya ga gwamnati da Majalisar dokoki ta amince da ita ta yadda za ta karfafa, sannan hanyar lumana da siyasa ce hanyar da za a warware rikicin na Libiya.

Sanarwar ta ce "Muna goyon bayan Libiya guda daya tak wadda farar hula ke jagoranta", inda ta kuma bukaci dukkan 'yan sanda da sojoji da su kasance karkashin umarnin wannan gwamnati.

A sanarwar an yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta kafa Kwamitin da zai tabbatar da an tsagaita wuta da kuma hanyoyin da za a bi wajen tabbatar da hakan, kuma an buka MDD da ta dauki nauyin saukaka hanyar da za a cimma matsayar sulhu.

Sanarwar ta kuma ce "Muna kira ga dukkan bangarori da su dakatar da aiyukan sojojinsu da zarar yarjejeniyar tsagaita wutar ta fara aiki."

Haka zalika sanarwar bukaci da 'yan kasar Libiya su dawo turbar Demokradiyya ta hanyar gudanar da zabe  wanda za a gudanar cikin adalci bisa tsari mai kyau.Labarai masu alaka