Mutane 87 'yan tawayen Houthi suka kashe a Yaman

Mutane 87 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da 'yan tawayen Houthi da Iran ke taimakawa suka kai kan sansanin sojin Yaman dake garin Ma'arib.

Mutane 87 'yan tawayen Houthi suka kashe a Yaman

Mutane 87 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da 'yan tawayen Houthi da Iran ke taimakawa suka kai kan sansanin sojin Yaman dake garin Ma'arib.

Majiyoyin soji sun ce sutane 87 ne suka mutu yayinda wasu 30 suka jikkata sakamakon harin da 'Yan tawayen Houthi suka kai sansanin soji dake garin Ma'arib na gabashin Yaman.

An bayyana cewar wasu daga cikin wadanda suka jikkata na cikin mawuyacin hali.

Shugabannin asibitin Al-Haya dake Ma'arib sun ce har yanzu ba a gano mafi yawan wadanda suka rasa rayukansu ba.

Majiyoyin soji dake da alaka da gwamnati sun ce an kai harin da makami mai linzami.

Bayanan da aka samu daga majiyoyin sojin sun kara da cewar sojojin gwamnatin Yaman sun kai hari kan mayakan Houthi da suka shirya kai musu farmaki a gundumar Nehem, kuma a arangamar da ta barke an kashe 'yan tawaye 23 da sojoji 3.Labarai masu alaka