Haftar ya ki sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Libiya

Shugaban Gwamnatin Hadin Kan Kasa ta Libiya Fayyaz Sarraj ya sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta amma Shugaban 'yan tawaye Janar Haftar Khalifa ya ki sanya hannu.

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya da ya ziyarci Rasha ya yi bayani game da halin da ake ci a Libiya a lokacinda suke gudanar da taron manema labarai da takwaransa Sergey Lavrov.

Cavusoglu ya ce "Mun samar da yarjejeniyar da za ta tabbatar da zaman lafiya. Mun kuma duba shawarwarin da bangaren Haftar suka bayar game da yarjejeniyar."

Ministan ya ci gaba da cewar bayan da aka kawo karshen lamarin ne Haftar ya bayyana musu cewar yana bukatar karin lokaci, amma Shugaba Sarraj ya sanya hannu tuntuni.Labarai masu alaka