Erdogan: Abun kunya ne yadda Haftar ya ki sanya hannu kan yarjejenir zaman lafiya

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewar dan juyin mulki Haftar Khalifa ya gudu daga Moscow Babban Birnin Kasar Rasha ba tare da sanya hannu kan yarjejeniyar da za ta kawo zaman lafiya tsakanin dukkan bangarori ba.

A yayin taron jam'iyyar AKP mai mulki a Turkiyya Shugaba Erdogan ya bayyana cewar Haftar ya gudu daga Moscow ba tare da sanya hannu kan daftarin yarjejeniyar ba.

Ya ce "Da Turkiyya ba ta sanya baki ba, da zuwa yau Haftar ya kwace dukkan sassan Libiya, da dukkan jama'ar Libiya sun fada karkashin zalunci."

Erdogan ya ci gaba da cewar "Mun cika alkawarinmu, bangarensu ya sanya hannu kan yarjejeniyar, yanzu ya rage na Rasha da bangarenta. Abin takaici ne yadda Haftar ya gudu daga Moscow ba tare da sanya hannu kan yarjejeniyar ba. Wakilan Turkiyya da suke wajen sun yi duk abunda ya kamata."

Ya ci gaba da cewar abunda Haftar ya yi na nuni da irin fuskarsa da kuma fada wa duniya shi waye.

Shugaba Erdogan ya kuma ce Turkiyya za ta ci gaba da bibiyar matakin da halartacciyar gwamnati da bangaren haftar za su dauka a Libiya.

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu kuma ya bayyana cewar idan har Haftar ba zai sanya hannu kan yarjejeniyar ba to taron da za a yi a Berlin ba shi da wani amfani.

 Labarai masu alaka