Iran ta bayar da hasken yiwuwar yin sulhu da Amurka

Shugaban Kasar Iran Hassan Ruhani ya bayar da hasken yiwuwar su yi sulhu da Amurka idan hakan zai kore tuggu da makircin kasar.

Iran ta bayar da hasken yiwuwar yin sulhu da Amurka

Shugaban Kasar Iran Hassan Ruhani ya bayar da hasken yiwuwar su yi sulhu da Amurka idan hakan zai kore tuggu da makircin kasar.

A jawabin da ya yi a Jami'an Malamai dake Babban Birnin Kasar Tehran ya bayar da hasken yiwuwar sake zama a teburin sulhu da Amurka.

Ruhani ya kuma ce yarjejeniyar Nukiliya da suka yi da Amurka tana farantawa kasarsa inda kafin a kulla ta suke fitar da albarkatun man fetur ganga miliyan 1 amma bayan amincwa da ita suke fitar da ganga miliyan 2 da dubu 800.

Ya ce "Makiya na matsa lamba. Iran kuma na mayar da martani. Idan sulhu zai karya makirci da tuggun makiyi to zai zama mataki mai kyau."

Da yake tabo zanga-zangar adawa da karin farashin man fetur a Iran, Ruhani ya ce duk da korafin mutane amma ya kamata su sani za su yi wa jama'a aiyuka da dukkan kudaden da za a samu.Labarai masu alaka