An jikkata sojojin Iraki 6 a wani harin makami mai linzami

Sojoji 6 ne suka jikkata sakamakon wani hari da makami mai linzami da aka kai a kusa da filin tashi da saukar jiragen saman Bagdad Babban Birnin Iraki.

Sanarwar da kafar yada labaran jami'an tsaron Iraki ta fitar ta ce an kai hari da makami mai linzami samfurin Katyusha kan sansanin soji dake kusa da filin tashin jiragen sama na Bagdad.

An jikkata sojoji 6 a harin.

An bayyana cewar a binciken da aka gudanar a yankin an gano wani waje da ake harba makamai masu linzami daga cikinsa.

A kwanakin da suka gabata an kai hare-haren makamai masu linzami kan sansanonin sojin Amurka a lardunan Salahaddin da Anbar dake Iraki.Labarai masu alaka