Isra'ila ta sake kama Falasdinawa 12 a Yammacin Gabar Kogin Jordan

Dakarun sojin Isra'ila sun kama Falasdinawa 12 da suka hada da yaro karami 1 a Yammacin Gabar Kogin Jordan da Yahudawa suka mamaye.

Isra'ila ta sake kama Falasdinawa 12 a Yammacin Gabar Kogin Jordan

Dakarun sojin Isra'ila sun kama Falasdinawa 12 da suka hada da yaro karami 1 a Yammacin Gabar Kogin Jordan da Yahudawa suka mamaye.

Sanarwar da Rundunar Sojin Isra'ila ta fitar ta ce, an kama Falasdinawan su 12 a yankuna daban-daban na Yammacin Gabar Kogin Jordan.

An kai Falasdinawan cibiyar tsaro ta Isra'ila don amsa tambayoyi.

Isra'ila na yawan kai farmakai a Yammacin Gabar Kogin Jordan da Gabashin Kudus inda take kama Falasdinawa da take zargi da yunkuri ko aikata ta'addanci, kuma mutanen da sukan hada da mata da yara kanana na daukar tsawon lokaci a hannun Isra'ila.

Akwai Falasdinawa sama da dubu 5 da suka hada da yara kanana 220 a gidajen kurkukun Isra'ila.

A karkashin wata dokar kama Falasdinawa, Isra'ila na iya daure su na tsawon wata 1 zuwa 6.

Idan kuma kotu ta bayyana mutumin da aka kama na barazana ga zaman lafiyar Yahudawa to za a iya daure shi har shekaru 5 a gidan maza.Labarai masu alaka