An kashe jami'an tsaro 2 a wani hari a Kabul

Jami'an tsaro 2 sun rasa rayukansu sakamakon harin da aka kai musu a Kabul Babban Birnin Afganistan.

An kashe jami'an tsaro 2 a wani hari a Kabul

Jami'an tsaro 2 sun rasa rayukansu sakamakon harin da aka kai musu a Kabul Babban Birnin Afganistan.

Kakakin Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida Nasrat Rahimi ya shaidawa 'yan jaridu cewar wasu da ba a san ko su waye ba ne suka kai wa jami'an tsaro farmaki a yankin Yaka Tutu na Kabul.

Rahimi ya ce an kashe jami'an tsaro 2 tare da jikkata wani daya a harin.

Rahimi ya kara da cewar maharan sun gudu daga yankin amma an fara yunkurin kamosu.

Ya zuwa lokacinda muke tattara labaran babu wanda ya dauki alhakin kai harin.Labarai masu alaka