An kashe jami'an tsaro 2 a wani hari a Kabul

Jami'an tsaro 2 sun rasa rayukansu sakamakon harin da aka kai musu a Kabul Babban Birnin Afganistan.

An kashe jami'an tsaro 2 a wani hari a Kabul

Jami'an tsaro 2 sun rasa rayukansu sakamakon harin da aka kai musu a Kabul Babban Birnin Afganistan.

Kakakin Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida Nasrat Rahimi ya shaidawa 'yan jaridu cewar wasu da ba a san ko su waye ba ne suka kai wa jami'an tsaro farmaki a yankin Yaka Tutu na Kabul.

Rahimi ya ce an kashe jami'an tsaro 2 tare da jikkata wani daya a harin.

Rahimi ya kara da cewar maharan sun gudu daga yankin amma an fara yunkurin kamosu.

Ya zuwa lokacinda muke tattara labaran babu wanda ya dauki alhakin kai harin.

Labarai masu alaka