Koriya ta Arewa ta gasgata yin gwajin makami mai linzami

Koriya ta Arewa ta gasgata cewar ta gwada harba makamai masu linzami 2 zuwa tekun gabashin kasar daga jihar Hamgyon ta Kudu.

Koriya ta Arewa ta gasgata yin gwajin makami mai linzami

Koriya ta Arewa ta gasgata cewar ta gwada harba makamai masu linzami 2 zuwa tekun gabashin kasar daga jihar Hamgyon ta Kudu.

Kamfanin dillancin labarai na Koriya ta Kudu ya rawaito bayanan da na Koriya ta Arewa ya fitar inda ya ce an gwada harba makaman a gaban Shugaba Km Jong-un.

A labaran an bayyana cewar an gwada harba makaman a wani bangare na gwajin makaman da jami'an tsaro take samarwa, kuma shugaba Kim ya bayyana gamsuwarsa.

Rundunar Sojin Koriya ta Kudu kuma ta ce makaman sun yi tafiyar kilomita 380, kuma wannan gwaji ba zai haifar da zaman lafiya a tsibirin ba.Labarai masu alaka