Iran ta sanar da kama 'yan leken asirin Amurka 8 a cikin masu zanga-zanga

Iran ta sanar da kama mutane 8 daga cikin masu zanga-zangar adawa da karin farashin man fetur wanda kuma ta ce jami'an Hukumar Leken Asiri ta Amurka CIA ne.

Sanarwar da Ma'aikatar Leken Asiri ta Iran ta fitar na cewa 6 daga cikin mutanen sun fita zanga-zangar bayan umarnin da CIA ta ba su inda wasu 2 kuma suka aike da wasu bayanai zuwa kasashen waje.

Sanarwar ta ce mutanen sun shiga siffar 'yan jaridu wanda suke karbar taimakon kudi daga hannun CIA.

Takunkumin tattalin arziki da Amurka ta saka wa Iran na jefa jama'ar kasar cikin halin kaka-nika-yi, wanda a ranar 15 ga Nuwamba suka fara zanga-zangar adawa da karin farashin man fetur har ninki 3 da gwamnati ta yi.

Masu zanga-zangar suna mamaye gine-ginen gwamnati, bankuna da kasuwanni.

Kungiyar Kare Hakkokin Dan Adam ta Amnesty International ta ce akalla mutane 143 aka kashe sakamakon zanga-zangar.

Tag: Amurka , CIA , Iran

Labarai masu alaka