An kashe sojojin Saudiyya 2 a iyakar Yaman

Saudiyya ta sanar da cewar an kashe sojojinta 2 a kan iyakarta da kasar Yaman.

An kashe sojojin Saudiyya 2 a iyakar Yaman

Saudiyya ta sanar da cewar an kashe sojojinta 2 a kan iyakarta da kasar Yaman.

Kamfanin dillancin labarai na Saudiyya SPA ya bayyana cewar Faris Said Al-Gamidi da Isa Al-Silmi dake aiki a kudancin Yaman sun mutu.

Ba a bayar da mukaman sojojin ba da kuma ta yaya da yaushe ne suka mutu.

Mayakan Houthi na yan kai hare-hare a iyakar Yaman da Saudiyya musamman a garuruwan Najran da Jazan inda suke nufar mayakan Saudiyyar.

 Labarai masu alaka