Netanyahu ya yi kira da a kara tsaurara wa Iran takunkumai

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi kira ga kasashen duniya da su tsaurara matakan takunkumi kan Iran da ta yi karya game da sarrafa Nukiliya.

A wani bayani na bidiyo da Netanyahu fa fitar ya bayyana cewar Iran ta yi wa duniya karya game da sarrafa Nukiliya da take yi.

Ya ce "Iran na ci gaba da boye aiyukan Nukiliyar da take. Kuma tana habaka sinadarin Yuraniyom da ya saba wa dokokin kasa da kasa."

Firaminista Netanyahu ya kara da cewar Iran na barazana ga Gabas ta Tsakiya da dukkan duniya baki daya.

Ya ce "Ina kira ga dukkan kasashen duniya da su goyawa Amurka da Isra'ila baya wajen kara tsaurara takunkuman tattalin arziki da aka saka wa Iran."

Wannan kalamai na Netanyahu sun ja hankali ganin yadda suka zo a lokacinda Iran ta hana masu sanya idanu na Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta duniya shiga masarrafarta.

A kwanakin baya ne Iran ta hana jami'an na sanya idanu shiga masarrafar Nukiliyarta ta Natanz bisa zargin ta samu wani abu da ba ta yadda da shi ba a jikin daya daga cikin masu sanya idanun.Labarai masu alaka