Alakar Amurka da Koriya ta Arewa ta sake tabarbarewa

Koriya ta Arewa ta bayyana cewar bayan da Amurka ta ayyana kasarsu a matsayin wadda ke taimakawa aiyukan ta'addanci a duniya, alakar diplomasiyyar dake tsakaninsu ta ragu.

Sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Koriya ta Arewa ta fitar ta ce a rahoton da AMurka ta fitar kan ta'addanci a 2018 ta sake ayyana gwamnatin Pyonyang a matsayin mai taimakawa aiyukan ta'addanci wanda hakan ya sake jefa alakarsu cikin rikici.

Sanarwar ta ce "Wannan ha'inci da zagi a lokacinda ake tsaka da tattaunawa. Kafar tattaunawa tsakanin Koriya ta Arewa da Amurka na kara toshewa."

A rahoton Amurka na 2018 ta bayyana cewar kasashen Iran, Sudan, Siriya da Koriya ta Arewa na taimakawa aiyukan ta'addanci a duniya.

A rahoton an bayyana cewar Koriya ta Arewa na barazana ga kasashe makotanta ta hanar mallakar Nukiliya sannan tana aikata kisan gilla a kan iyakokinta.Labarai masu alaka