Mata 17 ne suke zaman dabaro don neman a dawo musu da yaransu a Turkiyya

A yankin Diyarbakir na Turkiyya mata 17 ne suke zaman dabaro inda suke neman a dawo musu da 'ya'yansu da 'yan ta'addar aware na PKK suka yi garkuwa da su zuwa tsaunuka.

Iyayen mata na ci gaba da zaman inda suke son lallai a dawo musu da yaransu.

A kowacce rana adadin matan na kara daduwa kuma suna samun goyon baya.

Mutane d adama dake yankin na kai wa matan abinci da abin sha.

A ranar 22 ga watan Agusta ne Hajara Akar ta fara zaman dabaro kan cewar 'yan ta'addar PKK sun yi garkuwa da danta Mehmet Akar mai shekaru 22 zuwa tsaunuka.

A ranar 24 ga watan Agusta kuma sakamakon gwagwarmayarta sai ga dan nata ya dawo.Labarai masu alaka