Ana sake gudanar da zaben magajin garin Istanbul

A yau lahadi ne al'umman birnin Istanbul suka yi tururuwan zuwa rumfunar zabe domin zabar sabon magajin gari da zai ja ragamar mulkin birnin na tsawon shekaru biyar.

1223271
Ana sake gudanar da zaben magajin garin Istanbul

A yau lahadi ne al'umman birnin Istanbul suka yi tururuwan zuwa rumfunar zabe domin zabar sabon magajin gari da zai ja ragamar mulkin birnin na tsawon shekaru biyar.

A zaben Jam'iyyar Adalci da Ci Gaba watau AK Party wacce ta yi hadaka da Nationalist Movement Party MHP masu dan takara Binali Yıldırım da jam'iyyar Republican Peoples Party CHP wacce ta yi hadaka da Good Party masu dan takara Ekrem İmamoğlu, Saadet Party wacce keda dan takara Necdet Gökçınar da Vatan Party wacce ta tsaida dan takara Mustafa İlker zasu fafata.

A kananan hukumomi 39 dake birnin mutane miliyan 10 da dubu 560 da 963 ne zasu halarci zaben.

Za'a dai yi amfani da rumfunar zaben da aka yi amfani dasu a zaben ranar 31 ga watan Maris ba tare da wata sauyi ba, bugu da kari wadanda suka kai shekaru 18 bayan zaben watan Maris da sojoji ba zasu kada kuri'a ba sabili da wannan zaben da aka soke ne ake maimaitawa.

An dai fara zaben ne da misalin karfe 8:00 na safe agogon Turkiyya kuma za'a kammala zaben ne da misalin karfe 5:00

Kafafen yada labarai zasu iya fara sanar da sakamakon zaben ne bayan hukumara zaben kasar ta bayar da umurnin yin hakan.

Sanadiyar kalubalantar zaben ranar 31 ga watan Maris da jam'iyyar AK Party ta yi ya sanya hukumar zaben kasar soke zaben magajin garin a ranar 6 ga watan Mayu ta kuma yanke hukiunci sake gudanar dashi a ranar yau.Labarai masu alaka