Farmakan Tafkin Zaman Lafiya

Manufar ita ce zaman lafiya,
ta'addanci ake nufa

Hankulan Shugaba Trump da Pelosi sun gushe

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump da Shugabar Majalisar Wakilai 'yar jam'iyyar Democrat Nancy Pelosi sun nuna wasu halaye dake nuna hankulansu sun bar jikinsu.

Hankulan Shugaba Trump da Pelosi sun gushe

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump da Shugabar majalisar Wakilai 'yar jam'iyyar Democrat Nancy Pelosi sun nuna wasu halaye dake nuna hankulansu sun bar jikinsu.

Rikicin da ya fara bayan da Trump ya fara mayar da martani ga Pelosi kan zargin da ta yi masa na boye bayanan binciken da ake masa game da Rasha inda ya yi kalamai munana marasa dadin ji.

Pelosi a lokacin da Trump yake gana wa da wasu 'yan majalisun jam'iyyar Democrats a Fadar White House kuma yke mayar da martani ga batun binciken sa kan Rasha wanda hakan ya sanya aka katse taron, ta fadi cewar domin kyautatuwar Amurka akwai bukatar iyalan Trump su saka hannu game da halaye marasa kyau da yake nuna wa.

Shugaba Trump bai yi sanya ba wajen mayar da martani inda ya ce, Pelosi wawiya ce, ba ta da amfani kuma ba yadda ya san ta a baya ba, a yanzu ta rasa hankali da tunaninta.

Ita ma Pelosi ta fitar da sanarwa ta shafin Twitter inda ta mayar da martan ga Trump da cewar "A lokacin da ya fara nuna halayya tagari, idan ya fara nuna shi shugaba ne, to sannan zan fara tattaunawa da shi kan cigaban kasa, kasuwanci da sauran batutuwa."

Labaran da jaridun Amurka suka fitar na cewar manyan jami'an gwamnati da aka zaba na tuhumar hankalin junansu.


Tag: Trump , Pelosi

Labarai masu alaka