Erdoğan zai ziyarci Rasha

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan zai kai ziyara na musanman kasar Rasha a ranar 8 ga watan Afirilu.

Erdoğan zai ziyarci Rasha

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan zai kai ziyara na musanman kasar Rasha a ranar 8 ga watan Afirilu.

Mai magana da yawun fadar gwamnatin Rasha ta Kremlin Dmitriy Peskov ya bayyana cewar Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin zai gana da shugaban kasar Turkiyyya Recep Tayyip Erdoğan a babban birnin kasar Moscow sanadiyar babban taron 'yan kasuwa da za'a gudanar a ranar 8 ga watan Afirilu.

Wannan dai zai kasance ganawa ta biyu da shugabanin zasu yi a cikin wannan shekarar.

Shugabanin zasu kuma bude shirin "Shekarar Al'adu da Yawon bude ido ta Turkiyya-Rasha"

 Labarai masu alaka