Katar ta la'anci harin da aka kai a Masar

Ma'aikatar Harkokin Wajen Katar ta la'anci harin kunar bakin wake da aka kai a Alkahira Babban Birnin Kasar Masar inda aka kashe jami'an tsaro 2 tare da jikkata wasu 2.

Sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Katar ta fitar a rubuce na cewa,suna suka tare da la'antar wannan hari da aka kai a Alkahira, kuma a kowanne hali Katar ta ke tana da halayyar yaki da ta'addanci da dukkan nau'i na rikici.

Sanarwar ta mika ta'aziyya ga makusantan wadanda suka mutu da ma al'umar Masarbaki daya tare da Addu'ar samun suaki ga wadanda suka jikkata.

A yammacin Litinin din nan ne aka kai hari a bayan Masallacin Juma'a na Al-Azhar dake Alkahira inda aka kashe jami'an tsaro biyu tare da jikkata wasu 2.Labarai masu alaka