Sanarwar bayan taron Turkiyya, Iran da Rasha da aka yi a birnin Sochi

Bayan kammala taron da Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, Shugaban Rasha Vladimir Putin da na Iran Hassan Ruhani suka yi a birnin Sochi na Rasha game da Siriya an fitar da sanarwar bayan taron.

1145825
Sanarwar bayan taron Turkiyya, Iran da Rasha da aka yi a birnin Sochi

Bayan kammala taron da Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, Shugaban Rasha Vladimir Putin da na Iran Hassan Ruhani suka yi a birnin Sochi na Rasha game da Siriya an fitar da sanarwar bayan taron.

Sanarwar ta hadin gwiwa ta ce "Shugabannin sun dauki matakin adawa da 'Yan aware na Siriya."

Sanarwar ta ci gaba da cewa, shugabannin sun nuna muhimmancin da 'yancin Siriya da al'umarta yake da shi sannan sun ce, idan Amurka ta janye daga kasar gaba daya za a samu damar karfafar al'umarta tare da tabbatar da dawwamammen zaman lafiya.
Shugabannin na Turkiyya, Iran da Rasha sun amince da daukar kwararan matakan tabbatar da aiki da yarjejeniyar rage rikici a yankunan Idlib.

Sun kuma amince da ci gaba da yaki da ta'addanci ta hanyar hada kai a tsakaninsu.

Shugabannin sun kuma ake sabunta cewar daukar matakan soji ba za su kawo karshen rikicin Siriya ba amma idan 'Yan Siriya suka yi jagoranci wajen tabatar da tsarin da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin DUniya ya samar to shi ne za a samu zaman lafiya mai dorewa.

Shugabannin kasashen 3 da suka zama Garanton bangarori daban-daban na Siriya sun bukaci da a gaggauta kafa kwamitin da zai yi aikin samar da Kundin Tsarin Mulkin kasar.

Shugabannin sun kuma bayyana jin dadinsu game da yadda gwamnati da 'yan adawa suka saki mutanen da suka kama.

Sanarwar bayan taron ta kuma yi kira da a samar da tsare-tsaren da za su bayar da dama a kai kayan taimako zuwa Siriya ta hanyar amfani da Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyoyi Masu Zaman Kansu sannan a ba wa Siriyawa damar koma wa gidajensu.

Shugabannin sun amince da sake gudanar da taro na gaba a karo na 12 a Astana wanda za a yi a watan Afrilun bana.

An kuma amince da yin taron kasashen 3 a Turkiyya.Labarai masu alaka