Bunkasar dangantakar Turkiyya da kasashen Nahiyar Afirka

Ministan harkokin wajen kasar Turkiyya Mevlüt Çağuşoğlu ya gana da jakadodin kasashen nahiyar Afirka a Ankara babban birnin kasar Turkiyya inda anka tattauna akan akan bunkasar dangantakar Turkiyya da nahiyar tare da tabo batun taron kolin Turkiyya-Afrika

Bunkasar dangantakar Turkiyya da kasashen Nahiyar Afirka

Ministan harkokin wajen kasar Turkiyya Mevlüt Çağuşoğlu ya gana da jakadodin kasashen nahiyar Afirka a Ankara babban birnin kasar Turkiyya inda anka tattauna akan akan bunkasar dangantakar Turkiyya da nahiyar tare da tabo batun taron kolin Turkiyya-Afrikakaro na uku.

Kamar yadda anka rawaito daga ma'aikatun diflommasiyyar kasar minista Çavuşoğlu a  karin kumalo da taron haddin gwiwar da yake gudanarwa da jakadojin kasashen Afirka a Turkiyya  an tattauna akan harkokin ci gaban dangantakar dake tsakanin Afirka da kasar tare da kuma shirin gudanar da taron kolin Turkiyya-Afirka.

A taron jakadojin Afirka a Ankara babban birnin Turkiyya sun bayyana irin farin cikinsu da gamsuwarsu akan yadda kasar Turkiyya ke kokarin kolla hurda mai inganci da nahiyar Afirka. Bayan haka sun kuma sun bayyyan ra'ayoyinsu akan yadda za'a inganta dangantakar bangarorin biyu.

A 'yan lokutan da sunka gabata Turkiyya ta daura damarar inganta da fadada dangantakarta da kasashen nahiyar Afirka. A dayan barayin kuma daga bunkasa kasuwanci zuwa ilimi da tattalin arziki bangarorin biyu sun kara kwarin gwiwar hurdarsu.

Bayan bayyana shirin inganta hurdar nahiyar Afirka da sauran kasashe da Tarayyar Nahiyar Afirka ta yi a shekarar 2008 daga wannan shekarar zuwa 2014 Turkiyya ta kara inganta hurdarta da kasashen nahiyar. A yayinda take da ofisoshin jakadanci 12 kachal a shekarar 2002 a halin yanzu akwai kusan ofisoshin jakadancin Turkiyya 42 a kasashe daban daban a nahiyar Afirka.

Haka kuma kasar Turkiyya na shirin kara yawan ofisoshin jakadancinta zuwa 50 anan bada jimawa ba a nahiyar. Haka kuma a Ankara babban birnin Turkiyya yawan ofisoshin jakadancin kasashen nahiyar Afirka ya karu daga 10 zuwa 35.

A dayan barayin kuma a yayinda kasuwanci tsakanin Turkiyya da kasashen Afirka yake na dala biliyan 3.63 a shekarar 2003 a shekarar 2018 ya haura zuwa dala biliyan 20.

 Labarai masu alaka