Guterres: Ya kamata a nemi mafita kan sauyin yanayi a duniya

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da a dauki matakan da suka kamata kan sauyin yanayi tun kafin lokaci ya kure.

Guterres: Ya kamata a nemi mafita kan sauyin yanayi a duniya

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da a dauki matakan da suka kamata kan sauyin yanayi tun kafin lokaci ya kure.

An fara Babban taron Majalisar Dinkin Duniya Kan Sauyin Yanayi karo na 24 a garin Katoviche dake kudancin kasar Polan da bayanin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya da kuma Shugaban Kasar ta Polan Andrzej Duda.

A jawabin da Guterres ya yi ya ce, idan aka yi rashin nasarar magance matsalar ta sauyin yanayi, to tuddan kankara za su ci gaba da narkewa, tekuna da su cika makil da ruwa inda halittu da yawa dake cikin ruwan za su mutu.

Guterres ya yi nuni da cewar, dumamar yanayi a duniya zai kuma janyo mutane da dama su rasa rayuka da dukiyoyinsu, kuma za a fi samun asarar wajen mutuwar "Ozon layer" wani sinadari dake zuke tiririn rana wanda ke hana shi cutar da dan adam da duniyarmu.

Guterres ya ci gaba da cewa, akwai bukatar a yi aiki da yarjejeniyar da aka cimma a Paris, kuma Kasashe Mambobin Majalisar Dinkin Duniya na da alhakin kawar da "Rikicin Sauyin Yanayi".

Ya ce, "Har yanzu ana tafiyar wahainiya wajen daukar matakan magance matsalar sauyin yanayi a duniya."

Sakatare Janar din na Majalisar Dinkin Duniya ya kara da cewa "Sakamakon wannan matsala dole ne a dauki mataki cikin gaggawa. Tun tsawon lokaci sauyin yanayi ya illata mutane, kasashe da yankuna dake doron kasa."

Da yake tabo batun fitar da sinadarin Carbon da irin matakan da za a dauka, Guterres ya ce, nan da shekarar 20130 ana sa ran za a rage yawan iskar carbon da ake fitar wa a duniya gaba daya zuwa kaso 45 inda a shekarar 2050 kuma ake da manufar daina fitar da ita baki daya.

A nasa jawabin, Shugaban Kasar Polan Duda ya ce, yana da matukar muhimmanci kasashe Mambobin Majalisar Dinkin Duniya da su nuna a shirye suke wajen aiwatarwa tare da aiki da yarjejeniyar sauyin yanayi daka acimma a Paris.

Duda ya ja hankali da cewa, a wajen taron da zai dauki tsawon makwanni 2 za a samar da wani daftari dauke da hanyoyiin da za a bi wajen tabbatar da aiki da yarjejeniyar ta Paris.

A wajen taron na tsawon makwanni 2 da shugabannin kasashen duniya sama da 200 da kuma mahalarta sama da dubu ashirin suke halarta, zai kunshi tattaunawa kan aiki da yarjejeniyar da aka cimma kan sauyin yanayi a shekarar 2015 a Paris Babban Birnin Kasar Faransa.

Akarkashin yarjejeniyar ta Paris, ana da manufar daukar matakan kawar da dukkan matsaloli tattalin arziki da man takewa da sauyin yanayi yake janyowa daga bayan shekarar 2020. Manufar yarjejeniyar mai dogon wa'adi kuma ita ce a samu yanayin dumi a duniya daidai da na lokacinda ake rayuwa babu kamfanunnuka.

Domin cimma wannan manufa dole ne a daina amfani da man fetur ko a rage shi inda za a dinga amfani da makamashi mai sabntuwa.

A karkashin haka za a samar da kudade ga kasashe masu tasowa, kai musu fasahar kere-kere da hanyoyin ci gaba da damarnmakin rayuwa.

A ranar 14 ga watan Disamban nan za a fitar da sanarwar bayan taron idan an kammala shi.Labarai masu alaka