Turkiyya: Zamu ɗauki matakan siyasa domin kawo ƙarshen rikicin Siriya

Mai magana da yawun shugaban ƙasar Turkiyya lbrahim Kalin ya bayyana cewar Turkiyya zata dauki kwararan matakan siyasa akan hare-haren da ake kaiwa yankin ldlib.

A jawabin da ya yi a taron ƙolin ministocin kasar, lbrahim Kalin ya bayyana cewar za'a tattauna a kuma aminta da Amurka, kasashen yamma da sauran ƙasashen yankin domin dakatar da hare-haren kin ƙari da ake kaiwa ldlib.

Ya kara da cewa Turkiyya na cigaba da ganawa da sauran ƙasashe akan hare-haren da ake kaiwa Siriya.

Kalın, wanda ya bayyana cewar za'a dauki matakai masu kwari akan warware matsalolin Siriya ya kara da cewa hanyar siyasa ce magm muhimmanci domin kawo karshen rikicin Siriya.Labarai masu alaka