MDD za ta tattauna sakamakon taron da Turkiyya, Iran da Rasha suka yi kan Siriya

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai yi zama na musamman don duba sakamakon taron da Turkiyya, Iran da Rasha suka gudanar a ranar Juma'ar da ta gabata a Tehran game da halin da Idlib da Siriya baki daya ke ciki.

Bayanan da aka samu daga majiyoyin diplomasiyya na MDD na cewa, Rasha ce ta nemi ta sanar da Kwamitin Tsaron kan taron da suka gudanar.

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa, a cikin mako guda da aka dauka ana kai hare-hare a Idlib an raba mutane dubu 30 da gidajensu inda aka kashe wasu da dama.

A yayin taron da aka yi na kasa da kasa a Astana a tsakanin 4-5 ga watan Mayun 2017 an ayyana yankin Idlib da wasu yankunan arewa maso-yammacin Siriya a matsayin yankunan zaman lafiya.Labarai masu alaka