Za a gudanar da babban zabe a Bahrayn

Al'umar Kasar Baharayn za su fita don gudanar da babban zabe a ranar 24 ga watan Nuwamban bana.

Za a gudanar da babban zabe a Bahrayn

Al'umar Kasar Baharayn za su fita don gudanar da babban zabe a ranar 24 ga watan Nuwamban bana.

Kamfanin dillancin labarai na Bahrayn ya sanar da cewa, bayanan da Sarkin Bahrayn Hamed bin Isah Al-Khalifa ya fitar sun bayyana za a gudanar da zabe a ranar 24 ga watan Nuwamba. 

An bayyana za a karbi takardun masu son tsaya wa takarar 'yan majalisar dokoki a tsakanin 17-21 ga Oktoba.

'Yan kasar Bahrayn da ke kasashen waje kuma za su yi zabe a ranar 20 ga Nuwamba a ofisoshin jakadancin kasarsu da ke waje.

Wannan ne karo na 5 da cikin shekaru 16 da Bahrayn za ta gudanar da babban zabe.Labarai masu alaka