Kalin: Kai wa Idlib hari zai lalata kokarin samar da zaman lafiya a Siriya

Kakakin Shugaban Kasar Turkiyya Ibrahim Kalin ya bayyana cewa, ci gaba da kai wa yankin Idlib na Siriya hare-hare zai kawo cikas ga yunkurin samar da zaman lafiya da ake yi.

Kalin: Kai wa Idlib hari zai lalata kokarin samar da zaman lafiya a Siriya

Kakakin Shugaban Kasar Turkiyya Ibrahim Kalin ya bayyana cewa, ci gaba da kai wa yankin Idlib na Siriya hare-hare zai kawo cikas ga yunkurin samar da zaman lafiya da ake yi ta hanyar siyasa.

Bayan taron Majalisar Ministocin TurkiyyaKalin ya yi wa manema labarai inda ya yi kira ga Amurka, kasashen yankin da na yammacin duniya da su hada kai waje guda tare da kawo karshen rikicin na Idlib.

Kalin ya ce "Ya kamata a sani kafin komai rikicin Idlib zai lalata yunkurin samar da zaman lafiya ta hanyar siyasa da ake yi."

Kakaki Kalin ya ci gaba da cewa, suna sauraron ganin dukkan kasashe 'yan uwa sun dauki matakan ganin an kawo karshen rikicin Siriya, kuma suna sa ran za a dauki matakai na siyasa.Labarai masu alaka