An kama Malaman Shi'a 5 a Iran saboda barazanar za su kashe Shugaban Kasar

An kama wasu manyan Malaman Shi'a 5 a Iran sakamakon daga wasu alluna a wajen wani, taro a garin Kum da ke nuna yin barazanar kashe Shugaban Kasar Hassan Ruhani.

Fadar Shugaban Kasar Iran ce ta gabatar da korafi a kotu kan cewar Malaman sun yi barazanar kashe Shugaba Ruhani a wajen wani taron da daliban makarantar Fevziye suka shirya ta hanyar daga alluna tare da yin rubutu a jikinsu.

 jikin allunan an yi rubutu game da dalilin mutuwar tsohon SHugaban Iran Hashimi Rafsanjani tare da rubuta cewar "Ya kai mai yin yarjejeniya, wurin wanka yana jiranka."

Tsohon Shugaban Iran Rafsanjani ya mutu a wajen wanka a watan Janairun 2017.

Da fari an sanar da cewar, Rafsanjani ya mutu sakamakon bugun zuciya amma a watan Disamba 'yarsa ta ce, bai mutu ta hanyar dabi'a ba kuma rashin tabbas na ci gaba da gudana.

Wasu masu ra'ayin gyara na ganin an nufi Ruhani da wadannan alluna a lokacin da ake ci gaba da kulla alaka da Yamma kan barun mutuwar ta Rafsanjani.Labarai masu alaka