Erdogan ya gana da Ruhani da Putin a Tehran

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da ya ziyarci Tehran don gudanar da Babban Taro ya gana da Shugaban Kasar Iran Hassan Ruhani da Rasha Vladimir Putin.

erdogan ruhani.JPG

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da ya ziyarci Tehran don gudanar da Babban Taro ya gana da Shugaban Kasar Iran Hassan Ruhani da Rasha Vladimir Putin.

Da fari Shugaba Erdogan ya gana da takwaransa na Iran Hassan Ruhani.

Bayan nan ne kuma sai ya gana da Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin.

Bayan ganawar daya-daya sai kuma aka shiga gudanar da taro na su 3 baki daya.

A yayin Taron ana tattauna batun garin Idlib da ma Siriya baki daya. 

Bayan gama Babban Taron shugabannin za su gudanar da taron manema labarai.

Bayan Taron Shugaba Erdogan zai gana da Shugaban Addini na Iran Ayatullah Ali Hamaney.Labarai masu alaka