Diflomasiyya ita ce hanya mafi muhimmanci a yunkurin samar da lumana a Cyprus

Turkiyya wacce take amintattar ƙasa ta bayyana hanyar diflomasi a matsayar hanya mafi a’ala a yunkurin samar da lumana da ƙasa da ƙasa ke yunƙurin yi a Cyprus.

1015776
Diflomasiyya ita ce hanya mafi muhimmanci a yunkurin samar da lumana a Cyprus

A wannan hoton, rundunar sojan Turkiyya ne da tankokinsu ke halartar taron samar da lumanar Cyprus.

Turkiyya, ta kwashe shekaru 44 tana ɗaukar matakan samar da zaman lafiya,, walwala da kuma ƙare ƴancin al'umar Cyprus ta Hanyar Diflomasiyya tsakanin ƙasashen.

Da wannan hanyar diflomasiyya mai ɗorewa, rundunar sojan Turkiyya ta samar da lumana a tsibirin sanadiyar matakan da ta fara ɗauka a ranar 20 ga watan Yulin shekarar 1974.

Yanayin  da Cyprus take ciki gabanin matakan lumana.

Matsayin da Turkiyya da Girka suka aminta da shi a ranar 11 ga watan Fabrairun shekarar 1959, da kuma yarjejeniyar da Birtaniya da Cyprus suka rataɓawa hannu a Zurih da Landan akan samar da ƴanci da fitar da ƙasa biyu a Cyprus sun ta'allaka ne akan muhimmancin da ƙasashen Turkiyya, Birtaniya da Cyprus suka baiwa yunƙurin.

A sanadiyar yarjejeniyar ƙasa da ƙasa a shekarar 1960 an aminta akan ƙirƙirar Jamhuriyar Demokradiyyar Cyprus ta Turkiyya da kuma ta Girka a tsibirin akan daidaito da mutunta juna.

Saɓanin wannan tsarin, jamhuriyar dimokuraɗiyyar Cyprus ta Roma ta rinƙa kauracewa ta Turkiyya ta hanyar nuna banbanci inda kuma ta yi haɗaka da ƙasar Girka (Enosis)

Jamhuriyar Demokradiyyar Cyprus ta Roma, a shekarar 1963 ta yi watsi da dokar ɗaukar matakai bai ɗaya a tsibirin, a yayinda ta zaɓi aiyanar da lamurka ita tilo.

Rika ta rinƙa baiwa Enosis makamai domin ta cimma burinta, lamarin da ya bata damar fara kaiwa jamhuriyar dimokuraɗiyyar Cyprus ta Turkiyya hari da ƙalubalanta a shekarar 1974.

Lamurkan da suka sauya yunƙurin lumanar

Jamhoriyar demokradiyyar Cyprus ta Turkiyya ta fara tattaunawa da ta Roma a lokacin da Cyprus ta Roma ta fara ƙauracewa yarjejeniyar haɗaka tsakanin tsibiran biyu da aka aiyanar a shekarar 1960.

A sanadiyar rabuwar kawunan mambobin ƙungiyar EOKA, fita daga lamurkan Cyprus ta Turkiyya da kuma yunƙurin ƙalubalantar lamurkan tattalin arzikinta da shugaban Roma Makarios sun haifar da fara ƙalubalantar dakarun tsohuwar kungiyar EOKA-B

Tare da gudunmowar dakarun Girka, a ranar 15 ga watan Yuli 1974 shugaban dakarun EOKA Nikos Sampson ya kifar da gwamnatin Makarios a Girka da zummar mayar da ƴancin Cyprus karkashin Girka.

Yanayin Diflomassiya yankin gabanin matakan Turkiyya

Turkiyya ta kasance amintatciyar ƙasa musamman a fannonin zamantakewa da aiyuka tare a 1960.

A sanadiyar hakan ne, Turkiyya da Birtaniya suka gudanar da wata ƙawancen a Landan bayan juyin mulki tsakanin ranakun 17-18 ga watan Yuli 1974. A ƙawancen sun gaiyaci Girka sai dai gwamnatin sojan Girka bata halarci taron ba a wannan lokacin.

Firaministan wannan lokaci Bülent Ecevit da ministan harkokin Wajen Birtaniya na wannan lokaci James Callaghan sun tattauna  akan daukar matakan bai ɗaya akan yankin.

A yayinda Turkiyya ba ta aminta da hakan ba, ta mai da hankali akan tsaron Turkawan tsibirin, haka kuma ta mai da himma akan samar da lumana a Cyprus, a inda ta fara ɗaukar matakai a ranar 20 ga watan Yulin shekarar 1947.

A hakan ne aka kare matakan mamayar Cyprus da kuma samawa Turkawan tsibirin tsaro.

Da yin hakan, aka kawo karshen matakan samar da lumana da Turkiyya ke yi da ma lamurkan gwamnatin sojan Girka.

Ci gaban tattaunawar diflomasiyya kafin ƙaddamar da mataki na biyu.

A ranar 20 ga watan Yuli 1974 dangane da dokan majalisar tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya mai lamba 353 , Turkiyya ta yi kira ga a mutunta yunƙurin samar da lumana a tsibirin da Birtaniya da Girka suka jagoranta.

A dalilin hakan ne ,amintattun ƙasashen uku suka gudanar da taro a Geneva a ranakun 25-30 ga watan Yuli 1974 haka kuma ministocin harkokin wajen ƙasashen sun rattaba hannu a yarjejeniyar Geneva a ranar 30 ga watan Yuli 1974.

A yarjejeniyar an aminta da a ci gaba da yunƙurin samar da zaman lafiya a tsibirin da kuma dakatar da Girka da jamhuriyar Cyprus ta Roma daga mamayar yankin Turkawa cikin gaggawa.

Haka kuma yarjejeniyar ta aminta da samar da yanki biyu a tsibirin da suka haɗa da Cyprus ta Turkiyya da ta Roma.

 A karo na biyu na taron, wanda ya fara ranar 9 ga watan Agusta, Girka ta ƙi dukkan shawarwarin da aka kafa don kafa sabon tsarin mulki a cikin tsibirin, kuma ta ba da shawarar janye dakarun Turkiyya don bin hanyar sulhu a yankin.

An kammala taron a ranar 14 ga watan Agusta ba tare da cimma wata matsaya ba, Kuma kamar yadda lamurka suke a shekarar 1960 Girka ta ƙi amincewa da dukkanin mafitar da aka bayyana, akan hakan ne anka buɗe shafin ɗaukar matakin sulhun Cyprus na biyu.

Yunkurin da ya yi nasara daga bisani kuma anka kafa gwamnatin tarayyar Cyprus ta Turkiyya a ranar 13 ga watan Fabrairun shekarar 1975. A matakin da aka dauka a majalisa kuma an ka kafa jamhuriyar dimokuraɗiyyar Cyprus ta Turkiyya a ranar 15 ga watan Nuwambar shekarar 1983.

 

 Labarai masu alaka