An kashe mutane 12 a harin kunar bakin wake a Pakistan

Mutane 12 ne suka mutu inda wasu 35 suka jikkata sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai a wajen taron jam'iyyar ANP a garin Peshawer na Pakistan.

An bayyana cewa daga cikin wadanda suka mutu har da dan takarar majalisar dokoki Harun Bilur.'Yan sanda sun ce an kai harin a lokacinda Bilur ya ke ganawa da jama'arsa.

haka zalika daga jikin wadanda aka jikkata tare da kai su asibiti har da dan Bilur.

Har yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai harin.

Mahaifin Bilur Bashir Ahmad Bilur ma yarasa ransa a sheklarar 2012 a wajen wani taron casu da aka shirya a garin na Peshawer.

Kungiyar ta'adda ta Taliban ce ta dauki aihakin kai harin.Labarai masu alaka