Bai kamata dokar sanya Hijabi ta shafi 'yan yawon bude a Iran ba, inji wani Babban Shehi a Kasar

Wani Babban Malamin Kasar Iran Hujjatul Islam Muhsin Garuyan ya bayyana cewa, bai kamata dokar wajabcin sanya hijabi a Kasar ta shafi mata 'yan yawon bude ido ba.

Malamin Addinin ya yi jawabi ga jaridar "Business" inda ya ce, a mahanga ta Shari'a da Fikhu a Addini babu inda aka ce a takura wa 'yan yawon bude ido saka Hijabi ko dankwali.

Ya ce "'Yan yawon bude ido idan suna so su rufe kansu, a Addini ba dole ba ne su rufe".

Ya kara da cewa, idan Musulmai suka je Kasashen da ba na Musulmai ba muna yin yadda muke so ne, a saboda haka 'yan yawon bude ido ma kamata ya yi su yi yadda suke so.

Tag: Hijabi , Doka , Iran

Labarai masu alaka