Shugabannin Kasashen Duniya na ci gaba da taya Erdogan murna

Shugaban kasar Sloveniya Borut Pahor ya kira Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan tare da taya shi murnar nasarar lashe zaben ranar 24 ga Yuni.

Majiyoyoin Fadar Shugaban Kasar sun ce, Pahor ya kira Shugaba Erdoğan ta waya inda ya taya shi jurna sakamakon lashe zaben da ya yi wanda aka gudanar a ranar 24 ga watan Yuni.

An bayyana cewa sakamakon ganawar shugabannin biyu sun sake jadda za su kara karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashensu.

Shugaba Erdogan ya kuma tattauna ta wayar tarho da Shugaban Sairul Ittifak na Iraki Muktada Al-Sadr da kuma Firaministan Yankin Kurdawa mai zaman kansa da ke Irakin Narjiwan barzani.

Al-Sadr da Barzani sun taya Shugaba Erdoğan kjurnar nasarar lashe zaben na ranar 24 ga Yuni.Labarai masu alaka